Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu harin kunar bakin wake sun kashe farar hula 22 a Afghanistan


Sojoji da wata mace a lardi Kandahar
Sojoji da wata mace a lardi Kandahar

Jami'ai a kudancin Afghanistan sunce wasu masu harin kunar bakin wake sun kashe akalla farar hula ashirin da biyu a yau Laraba.

Jami'ai a kudancin kasar Afghanistan sunce wasu masu harin kunar bakin wake sun kashe akalla farar hula ashirin da biyu a kusa da sansanin kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Hukumomi sunce wasu masu harin kunar bakin wake guda biyu su kai hari wajen ajiye manyan motoci da direbobinsu suna jira su shiga sansanin a yau Laraba a lardin Kandahar. Mai harin kunar wake na farko akan babur shi ya fara tada bam na farko.

A yayinda mutane ke kokarin taimakon wadanda tashin bam din ya rutsa dasu, sai kuma mahari na biyu wanda ke tafiya ya tada bama bamai kusa da wasu kanan shaguna.

Akalla mutane hamsin ne suka ji rauni a wannan hari da aka kai kusa da wani sansanin kungiyar NATO

Kungiyar Taliban tayi ikirarin cewa ita keda alhaki kai hare haren. A yau Laraba kungiyar NATO ta zargi ita kungiyar Taliban da laifin ci gaba da karkashe farar hula, tana mai fadin cewa matakan da kungiyar ko dauka ko kuma take takenta suna jawowa diyaucin kasar Afghanistan barazana

A can gabashin kasar Afghanistan kuma, jami'an kasa sunce hare haren da kungiyar NATO da jiragen saman yaki sun kashe farar hula goma sha takwas ciki harda yara da mata a lardin Logar. Hoton vidiyon wurin da aka dauka ya nuna gawarwarkin mata da yara da aka loda bayan wata mota.

Kungiyar NATO tace ta fara bincike zarge zargen da ake yi cewa an jikatta farar hula, tana mai fadin cewa bata dauki zarge zargen da wasa ba.

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya sha yin kaca kaca da sojojin kasashen waje da laifin kashe farar hula. A makon jiya ya bada umarnin a gudanar da bincike harin da sojojin kawance suka kai da jiragen saman yaki daya kashe iyalin mutum takwas a lardin Paktia dake gabashin kasar

XS
SM
MD
LG