Accessibility links

Masu Ilimin Kimiyya Suna Kyautata Zaton Samun Maganin HIV


Dakin binciken cutar HIV

Shekaru talatin bayan bullar kwayar cutar HIV, masu ilimin kimiyya sun hakikanta cewa, yana yiwuwa a sami maganin cutar kanjamau wadda tayi sanadin kashe kusan mutane miliyan talatin.

Shekaru talatin bayan bullar kwayar cutar HIV, masu ilimin kimiyya sun hakikanta cewa, yana yiwuwa a sami maganin cutar kanjamau wadda tayi sanadin kashe kusan mutane miliyan talatin.

Kwararru sun bayyana cewa, ko da yake ba lallai a iya samun maganin da zai zama da taimako ga dukan wadanda suke dauke da cutar ba, mai yiwuwa ne a iya jinyar wadanda basu dade da kamuwa da cutar ba, da zai hada da maganin kara garkuwar jiki.

An yi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan talatin da hudu ne suka kamu da cutar a duniya kuma wajen mutane miliyan daya da dubu dari takwas suna mutuwa a shekara.

Kwararru sun bayyana cewa, mutanen da cutar ta dade a jikinsu ba lallai ne maganin ya zama da amfani a wurinsu ba. Sun kuma bayyana cewa yana da wuya wanda ya kamu da tarin fuka da kuma ciwon nemoniya ta dalilin cutar kanjamau.

Ana anfani da magungunan kashe kaifin kwayar cutar kanjamau yadda wanda yake dauke da kwayar cutar zai iya ci gaba da rayuwa ba tare da yawan kwanciya da rashin lafiya ba, ya kuma rage yada cutar, sai dai yawancin kwayar cutar tana boyewa ne jiki ta sake bayyana idan mutum ya daina shan magani.
XS
SM
MD
LG