Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Okada Sun Fara Yajin Aiki A Jihar Legas


Baburan haya, Okada

Masu sana'ar Okada a birnin Legas, wadanda yawancinsu daga jihohin arewa suka fito, sun shiga yajin aiki saboda a cewarsu 'yan sandan jihar na tursasa musu tare da tatsarsu kudade na ba gaira ba dalili.

Masu haya da babura da aka fi sani da 'yan Okada a birnin Legas sun fara wani yajin aiki na sai "baba ta gani" sanadiyyar matakin da rundunar 'yan sandan jihar ta dauka na fara kam asu muddin ba su bi wasu ka'idoji ba.

Rundunar ta bukace su, da su rika sanya wasu kaya da hula da kuma biyan wasu kudade. A cewar 'yan kungiyar Okadan da akasarinsu 'yan asalin jihohin arewa ne, jami'an 'yan sandan na musguna musu tare da karbar kudade a duk lokacin da suka ga dama.

Wani dan Okada ya ce dokar sa riga da hula tare da yankar tikiti basu ki ba amma bayan sun sa hula da riga sun yanki tikiti, yan sanda zasu gansu su kuma kamasu. Ya ce idan mutum ya yi magana sai dan sanda ya soma duka. Wani lokacin ma da motarsa zai sa ya buge mutum kana ya ce ya kamaka shi.

Amma a cewar rundunar 'yan sandan ta dauki matakan ne domin inganta harkokin tsaro a birnin na Legas. Duk da abun da 'yan sandan suka ce, 'yan Okadan basu gamsu ba saboda wai ana zaluntarsu.

A saurari cikakken bayani a cikin wannan rahoto na Babangida Jibrin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG