‘Yan raji masu muradin dimokradiyya a Hong Kong sun tattaru a wajen wani karamin ofishin jakadancin Amurka a birnin yau Lahadi a yayinda suke kokarin ganin kasashen duniya sun matsawa Beijing lamba biyo bayan watanni ukkun da aka kwashe ana zanga-zanga, da wani lokaci ma take rikidewa ta koma tarzoma.
Miliyoyin jama’a sun hau kan titunan Hong Kong a cikin makonni 14 kenan suna zanga-zanga, wani abu da ya zama kalubale mafi girma ga China tun bayan da Burtaniyya ta mika mata yankin a shekarar 1997.
An dai fara wannan zanga-zangar ne sakamakon wani mataki da yanzu ma aka soke, wanda ya amince a kai masu manyan laifuka China don su fuskanci shari’a, abinda ‘yan adawa suke gani kamar wani mataki ne na Beijing na kwace ‘yancin yankin mai cibiyar hada-hadar kudade ta kasa-da-kasa.
Dumbin mutane, wasun su dauke da tutar Amurka sun tattaru a wani fili a birnin na Hong Kong daga nan suka tattaka zuwa wani karamin ofishin jakadancin Amurka dake kusa. Suna yin kira ga shugaban Amurka Donald Trump akan ya taimaka ya ‘yantar da birnin.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 08, 2023
An Kama Wani Likitan Da Ya Yada Cutar Sankarau A Mexico
-
Fabrairu 06, 2023
Wata Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane Akalla 5,000 A Turkiyya Da Siriya
-
Fabrairu 04, 2023
Amurka Ta Kakkabo Babban Balan-Balan Na Leken Asirin China
-
Janairu 31, 2023
Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya
-
Janairu 30, 2023
Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan
Facebook Forum