Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga A Hong Kong Sun Tattaru A Tashar Jiragen Saman Birnin


Masu zanga-zanga dake muradin dimokradiyya a Hong Kong sun tattaru a wata tashar motocin bas dake tashar jiragen saman birnin don su gudanar da wani gangamin.

Hukumomi, a halin da ake ciki, sun dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa zuwa tashar jiragen saman. Ko da yake jiragen kasa daga tashar zuwa wasu wurare na ci gaba da aiki.

A yayin da hukumomi a Hong Kong ke nazarin asarar da aka yi cikin daren jiya sanadiyar masu adawa da gwamnati, jami’ai sun kare matakan da ‘yan sandan suka dauka a yayinda birnin ya turnike da hayaki, ya kuma cika makil da matasa da ke gwagwarmayar neman sauyin dimokradiyya.

A yayinda masu zanga-zangar suka dinga jifar ‘yan sandan da duwatsu, da wasu ababen fashewa da kuma toshe hanyoyi, ‘yan sandan sun maida martani da barkonon tsohuwa da kuma wata mota mai feshin ruwa, da duka, akwai lokacin da ma suka harba bindigogin gaske.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG