Masu jagorantar zanga-zanga a Sudan, sun ce za su ci gaba da zanga-zanga a birnin Khartoum, tare da yin banza da bukatar shugabannin mulkin sojin kasar ta su kawo karshen zanga-zangar, su kuma kau da shingayen da su ka kakkafa a kan hanyoyi.
Wata kungiyar kwararru kan harkoki daban-daban a kasar Sudan, wadda ke jagorantar zanga-zangar, ta bayyana jiya Litinin cewa za a ci gaba da zaman dirshan har sai an kafa gwamnatin farar hula.
Kungiyar na kiran da a yi maci na nuna bijirewa a yau dinnan Talata, sannan kuma ranar Alhamis a yi wani babban gangami.
A ranar Litinin masu zanga-zangar da kansu su ka rika aikin duba ababen hawa a kan hanyoyin da ke inda su ka yi tunga, a hedikwatar sojin kasar da ke birnin Khartoum.
Majalisar Mulkin Sojin Sudan ta yi kiran da a gaggauta bude hanyoyi, da kuma kawar da shingaye a inda masu zanga-zangar su ka yi tunga.
Facebook Forum