Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga Sun Kona Gidan Hakimin Bokkos

Gidan Hakimin Bakkos Da Aka Kona, Janairu 05, 2024
Gidan Hakimin Bakkos Da Aka Kona, Janairu 05, 2024

Rahotanni sun nuna cewa, kona gidan basaraken ya biyo bayan kisan gillar da aka yi a jajibirin Kirsimeti da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 160.

A wani yanayi na nuna bacin rai, wasu fusatattun mutane, galibin su mata, sun kona gidan Hakimin garin Bokkos, Monday Adanchi.

Mutanen yankin da su ka fusata na zargin Adanchi da yin watsi da su a cikin mawuyacin lokaci da ake fama da kashe-kashen mutane a wasu sassan karamar hukumar ta Bokkos da ke jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa, kona gidan basaraken ya biyo bayan kisan gillar da aka yi a jajibirin Kirsimeti da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 160.

Mata Masu Zanga Zanga A Bakkos Sun Kona Taya
Mata Masu Zanga Zanga A Bakkos Sun Kona Taya

Zanga-zangar dai ta faru ne da sanyin safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Janairu, 2024.

Matan da su ka gudanar da zanga-zangar sun bayyana kokensu, kan yadda aka tsare wasu matasa, biyo bayan gano gawar wani mutum a wata unguwa a garin na Bokkos.

Matan da suka yi zanga-zangar sun zarce zuwa gidan Hakimin, bayan sun lura da rashin zuwansa ofishin 'yan sandan, sai suka yi ta jifa, inda daga bisani suka kona gidansa tare da kone motoci biyu.

GIdan Hakimin Bakkon Da Mata Masu Zanga-zanga Suka Kona, Janairu 05, 2024
GIdan Hakimin Bakkon Da Mata Masu Zanga-zanga Suka Kona, Janairu 05, 2024

Jami'an tsaro sun yi gaggawar kwantar da tarzomar don hanata yin kamari a tsakanin al'umma.

Matan sun kuma nuna rashin jin dadi kan yadda hukumomi ke tafiyar da al’amuran tsaro da kuma yadda hukumomin kananan hukumomi da na tarayya su ke yin sakaci da batun tsaro a yankin.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su ce kome kan batun ba.

Bidiyo: Yadda Aka Kona Gidan Hakimin Bokkos (1).mp4
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG