Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Maharba Sun Soma Shiga Daji Domin Yaki da Boko Haram


Hajiya Habiba Isa Zing shugabar maharba mata

Yayinda maharba maza ke taimakawa wajen yaki da 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya su ma matan yankin ba'a barsu a baya ba domin mata maharba sun fito suna bada tasu gudummawar tare da shiga daji domin farautar 'yan ta'adda.

Kawo yanzu dai akwai mata da dama da suka sadaukar da rayukansu domin bada tasu gudumawa a yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram baya ga tallafin da suke badawa wajen tabbatar da tsaro da yaki da bata gari.

Su dai matan yan sakai na maharba sun ce,ba gudu ba jada baya musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da matsalolin tsaro kama daga na yan Boko Haram,da barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Mata Maharba
Mata Maharba

Domin baya ga Aisha Gombi,kwamandan maharba mata a shiyar arewa maso gabas,yanzu haka wata jarumar da ake fafatawar da ita itace Hajiya Habiba Isa Zing dake wakiltar jihar Taraba.

Habiba Isa Zing tace ta shiga wannan fafutukar ne domin ganin halin da jama’a ke ciki game da matsalar Boko Haram,wanda tace suma mata akwai rawar da zasu taka.

Kamar sauran yan sakai na maharba maza suma matan kan fada matsaloli da dama. Aisha Bakari Gombi dake jagorantar mata da maza a fagen yaki da yan Boko Haram ta ce su ke tara taro sisi su dauki hayar motoci don wannan aiki.

A can baya 'yan sakai na maharba ko yan sintiri da aka fi sani da yan banga kan taka muhimmiyar rawa wajen yaki da bata gari,koda yake da alamun an yi watsi da su, batun da masana ke ganin shi ya jawo tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya.

Mallam Sanusi Baba Fari wani mai sharhi da fashin baki ne kan harkokin tsaro a jihar Taraba,ya bayyana irin rawar da mata 'yan sakai ka iya takawa.

Ko ma da menene dai yanzu an zura ido aga irin tallafin da gwamnatocin wadannan jihohi zasu baiwa irin wadannan yan sakan da yanzu suka hada da mata.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG