Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Yunkuro A Jahar Adamawa


A'isha Alhassan, wata fitacciyar 'yar siyasa a Najeriya

Alamu na nuna cewa za a dama da mata a siyasar Adamawa, yayin da wasu daga cikin su su ka lashe zabukan fidda gwani

Da alamun dai a wannan karon mata sun yunkuro don kwace goruba a hannun kuturu inda a jihar Adamawa, mata da dama su ka haye zaben fidda gwanaye a jihar, domin baya ga wata tsohuwar jami’ar jinya da ta lashe zaben takarar gwamna a inuwar jam’iyar PPN, Mrs Lami Musa; an kuma samu mata ‘yan takara da suka lashe takarar neman kujerar Sanata da su ka hada da Sanata Binta Masi Garba, da kuma Aisha Dahiru Binani.

Ita dai Binani da ta kada wasu gangan yan siyasa biyu da suka hada da tsohon shugaban kungiyar shugabanin kananan hukumomin Najeriya ALGON, reshen jihar Barr. Aliyu Wakili Boya, da kuma tsohon shugaban hukumar kula da tasoshin ruwan Najeriya NPA, Engr. Omar Suleiman.

To sai dai kuma yayin da mata ke murna, har yanzu dai tana kasa tana dabo game da batun kujerar takarar gwamna na jam’iyar APC a Adamawa, Inda ake kai ruwa rana a Abuja. Dr Mahmud Halilu Ahmad yace suna nan daram sai sunga abun da ya turewa buzu nadi.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG