Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Suna Iya Kare ‘Ya’yansu Daga Kamuwa Da Malariya


Wata mata ta kai yaro asibiti

An shawarci mata a jihar Osun, su dauki kwararan matakai domin kiyaye ‘ya’yansu daga kamuwa da zazzabin cizon sauro

An shawarci mata a jihar Osun, su dauki kwararan matakai domin kiyaye ‘ya’yansu daga kamuwa da zazzabin cizon sauro.

Kwamishinan lafiya, Dr. Olaokun Soyinka, ya bada wannana shawara a taron da ma’aikatar lafiaya ta shirya, tare da hadin guiwar kungiyar Reckit Benckinser, yayin bukin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya.

Soyinka yace, wannan zai samu ne idan iyayen suna sa yaransu su kwana a karkashin gidan su kuma lura da kewayensu. Bisa ga cewarshi, sauro ba zai iya haduwa ba idan muhalli da tsabta.

A cikin nashi bayani, shugaban Reckit Benckinser, Mr. Ashok Bhashin yace, kungiyarsa na shirye ta hada hannu da gwamnati domin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG