Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan majalisar dokoki sun nemi yin Gwajin cutar kanjamau ga duk masu yin aure


Inda ake gwajin cutar kanjamau

‘Yan majalisar dokoki na jihar Bauchi suna kokarin fito da wata doka, wadda ta zama dole ga masu yin aure suje asibiti domin gwajin cutar kanjamau.

‘Yan majalisar dokoki na jihar Bauchi suna kokarin fito da wata doka, wadda ta zama dole ga masu yin aure suje asibiti domin gwajin cutar kanjamau.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya buga rahoto cewa, dan majalisa Ilyasu Zwall, wanda ke wakiltar Yankin Lere/Bula ne ya gabatar da bil din a zauren majalisa. Tuni kuma aka yi karatu na farko da na biyu.

Bisa ga cewar dan majalisa Ilyasu, idan akaamince da wannan bil, za’a bukaci masu shirin aure suje kowanne asibitin gwamnati da suka zaba domin a gwada su mako daya kafin ranar da za a daura masu aure.

Zai kuma zama dole ma ga masu mata idan zasu kara aure, suma suje ayi masu wannan gwaji.

Dan Majalisar yace yayi wata shida yana neman bayanai daga jama’arsa, kamar su shugabannin addini, na kauyuka, na lafiya, da kungiyoyin jiha dake aiki bisan cutar kanjamau, kafin wannan bil ya samu.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG