Wata baiwar Allah, Malama. Hauwa’u, tayi kira ga mata ‘yan uwanta da su tashi tsaye su tai makama kawunan su kamin ace masu gida jensu sun tallafa musu. Ganin cewar yau da gobe sai Allah. Ita dai wannan baiwar Allah ta dauki niyyar taimaka ma kanta kami ace mijinta yayi mata da ‘yayan ta harma da 'yan uwanta.
Ta dukufa ta koyi sana’a wadda take dogaro da ita, ita dai tana sana’ar dinka kayan kyale-kyale na sawa a dakuna don kawatar da daki. Tafara wannan sana’ar tun tana karatu a jami’a wanda ayanzu take yi kuma take taimakama 'yan uwanta. Takuma yi kira ga mata ‘yanuwanta da su tashi tsaye wajen sana’a wanda ba dole sai sun nemi bashi ba suna iya farawa da kadan kadan har su zo su zama masu taimaka ma wasu suma.
Tace mata su tashi su maida hankali wajen sana'o'i kowane iri, ba sai wada take kawo kudi dayawa ba a lokaci daya. Wannan shine kawai hanyar da zasu bi don magance matsalolin dake addabar kasar baki daya.