Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MATA: 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Amurka Sun Lashe Kofin Duniya


'Yan wasan kwallon kafa na Amurka mata suna murnar lashe kofin duniya

Wata alama ta baya-bayan nan dake nuna yadda ake samun Karin sha’awar kwallon kafa a Amurka itace daruruwan magoya baya, Amurkawa da suka tattaru a wajen fadar White House daren jiya lahadi don murnar nasarar da ‘yan wassan kwallon kafa na mata na Amurka suka samu inda suka doke Japan.

“Muna yin wani dan buki ne a fadar shugaba Obama” a cewar Wani ba’Amurke, dan kallon wassan kwallo, Mr. Donald Wine. Ya kuma bayyana gangamin ‘yan wasan a matsayin mafi girma da aka taba yi a wajen fadar shugaban Amurka, akala a cikin shekaru 10.

Mr. Wine ya shugabanci kungiyar da bata da wata kariyar dokar kasa, ba kuma ta neman riba ba, reshen Washington na nan Amurka – kungiyar dake goyon bayan kungiyoyin wassan kwallon kafa na Amurka. Karamin reshen da ake kira AODC, shine mafi girma a rassa 174 na kungiyoyin, wadanda ke da membobi fiye da 30,000.

Mr. Wine ya yi kiyasin cewa reshen AODC ya janyo kusan mutane 500 zuwa wajen kaddamar da bude wani wurin hutawa dake gundumar Columbia don kallon wasan kwallo, inda mata ‘yan wassan Amurka suka kara da takwarorinsu daga kasar Japan a karawar karshe. Amurka dai tayi nasara da ci 5 inda Japan ta shi da 2, yawancin rabin ‘yan kallon da suka je mashayar barasar, sun dunguma kan titi suna waka yayinda suka doshi fadar shugaban Amurka, don wurin ba shi da nisa da inda suke.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG