Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakan Firai Ministar Birtaniya Sun Fara Shirin Kamfe Na Ko Ta Kwana


Firai Ministar Birtaniya Theresa May a yayin da take bada jawabin daidaitawa a taron koli na tarayyar turai a 10 Downing Street, in London, Sept. 21, 2018.

Ko Theresa May zata iya tserar da Brexit daga cikin tsaka mai wuya?

Kafar dillancin labarai ta Reuters ta rawaito hadiman Firai Ministar Birtaniya Theresa May, sun fara shirye shiryen ko ta kwana na kamfe din zabe wanda za’ayi a watan Nuwamba, domin ta tsira da aikinta da kuma shirin fitar Birtaniya, daga tarayyar turai a wani rahoto da Jaridar Sunday Times ta wallafa.

Jaridar ta ce, manyan jami'an biyu na siyasa dake ofishin Firai Ministar a Downing Street, sun kaddamar da shirin atisayen kamfe din zaben domin samun nasarar goyon bayan al’umma a sabon shirin, bayan an caccaki shirin da ta mika na fitar Birtaniya daga tarayyar turai a taron kolin da akayi a Salzburg, a makon da ya gabata.

Ya zuwa yanzu ofishin Firai ministar bai ce komai ba game da wannan rahoto.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG