Adamu Ibrahim mataimakin babban sifeton 'yansandan Najeriya ya kira gwamnatin Jihar Ogun da ta kafa wata hukuma ta musamman da zata takawa masu magudin kwace filayen jama'a birki tare da hukumtasu.
Mataimakin ya bada shawarar ce yayinda ya kai wa gwamnan Ogun Ibikunle Amosun ziyara a ofishinsa dake Abeokuta babban birnin jihar. A cewarsa hukumar zata takawa masu yaudarar mutane suna kwace masu filaye birki. Yawancin masu yin hakan daga jihohin dake makwaftaka da Ogun suke fitowa.
Inji Adamu Ibrahim masu magudin kwace filaye suna shirin kwararowa jihar amma idan aka kafa hukumar da zata dauki matakai a kansu, zasu yi takatsantsan saboda hukumar zata hanasu cin karensu babu babbaka.
Mataimakin babban sifeton ya mika kokon bararsa ga gwamnatin jihar inda ya bukaci a sayawa 'yansandan jihar jiragen ruwa masu bindigogi da zasu dinga anfani dasu kan rafuka da ke jihar tare da tekun dake bangaren jihar domin shawo kan masu aikata laifuka.
Gwamnan jihar Ibikunle Amosun ya ce gwamnatinsa zata taimakawa rundunar 'yansandan da kayan aiki saboda suna aiki da jama'ai da shugabannin 'yansandan. Shi ma gwamnan ya nemi taimakon 'yansandan kan masu aikata aika aika kan ruwa a cikin jihar.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum