Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Jakadan Amurka A Najeriya Ya Jaddada Muhimmancin Karfafa Tsaro


Harin da aka kai Bawar Daji
Harin da aka kai Bawar Daji

Mataimakin Jakadan Amurka a Najeriya David Young yayi tsokaci game da yadda halin tsaro ya kasance a Najeriya inda mutane da dama ke rasa rayukansu.

Jakadan ya zagaya jihohin Zamfara da Kaduna, inda ya ce tashe-tashen hankula bai tsallake kowa ba- da makiyaya, da manoma, da kabilu mabanbanta, da musulmi da kirista dukkaninsu wannan rikici ya rutsa da su.

Ya ce ya fahimci cewa lallai wannan lamari ne mai rikitarwa kuma babu maslaha kai tsaye cikin sauki amma hanyar da suke ganin za ta iya zama mafita ita ce hada karfi da karfe domin murkushe dukkan mutanen da ke tayar da fitintinu ta yadda duk wanda aka kama da laifi doka za ta yi aiki akanshi.

Jakadan ya ce suna sane cewa gwamnati na kokari matuka amma saboda irin asarar rayukan da ake samu akwai bukatar gwamnati ta kara kwazo.

Young, ya ci gaba da cewa akwai bukatar kirkiro ayyuka na ci gaba domin samarwa matasa aikin yi kuma a cewarsa, sanin muhimmancin wannan ne yasa Amurka ta hada gwiwa da Najeriya wajen inganta fannonin ilimi, da lafiya, da tattalin arziki da noma da sauran bangarorin da zummar samar da aikin yi ga matasan kasar domin basu kwarin gwiwar kyautata makomarsu don gujewa zama bata-gari.

Ha-kazalika, jakadan ya ce ba zai yi wa tsaro a garuruwan Zamfara, da kudancin Kaduna, da Filato, da Borno, da Benue cinikin goro ba, domin ya fahimci cewa akwai banbance-banbance. Amma duk da haka akwai bukatar taimakawa mahukuntan a bangaren tsaro a kokarinsu na tabbatar da tsaro.

Ana sa ran wannan ziyarar da jakadan ya kai zai kara kyautata alakar Amurka da Najeriya, musamman wajen tabbatar da zabe na gaskiya da kuma inganta tsaro a kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG