Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakai Shida na Rage Hadarin Kamuwa da Cutar Kansa


Wajen kula da masu fama da cutar kansa
Wajen kula da masu fama da cutar kansa

A goshin ranar cutar kansa ta duniya, - Kungiyar Health-e – na kawo maku abubuwa shida da zaka iya chanzawa a rayuwarka domin rage hatsarin kamuwa da ciwon kansa daga shahararren masanin cutar kansa Dr Vikash Sewan na Afirika ta kudu.

A goshin ranar cutar kansa ta duniya, - Kungiyar Health-e – na kawo maku abubuwa shida da zaka iya chanzawa a rayuwarka domin rage hatsarin kamuwa da ciwon kansa daga shahararren masanin cutar kansa Dr Vikash Sewan na Afirika ta kudu.

Yawancin cututtukan kansa cututtuka ne da za’a iya karewa. Dr. Vikash Sewram, direkton sashin cutar kansa a Afrika na Jami’ar Afrika ta Stellenbosch ya bamu matakai shida da zaka dauka yanzu domin rage hadarin cutar kansa.

Kada ka sha taba – shan taba na kawo kashi 33 daga cikin dari na dukan cututtukan kansa.

Kiyaye kanka daga yawan hasken rana – dukan mutane, ba marasa launin fata kadai ba, suna bukata su rage yawan lokacin da suke kashewa a cikin hasken rana, idan har zasu dade a waje, to su sa kayan da zai rufe su daga hasken rana.

Rage shan giya – yawan shan giya na kawo cutar kansar baki, makogoro, wurin magana, hanta da mama.

Yi amfani da abinci mai lafiya – ka ci kayan itatuwa da rage cin abu mai kitse.
Ka lura da kibar ka kuma ka motsa jiki sosai – yawan kiba sosai yana kara hatsarin kamuwar cutar kansar mama, mahaifa, koda, aya biyu da kansar golaye kuma tana rage damar da kake da ita ta rayuwar.

Duba jiki akai akai – da mace ta kai shekaru 21, ya kamata ta rika yin gwajin gabanta (wani gwaji da ake kira pap smear) bayan kowace shekara uku, idan kuma ta kai shekaru 40, ta rika yin gwajin mama sau biyu a shekara. Maza dake tsakanin shekara 40 zuwa 70 suna bukata su rika zuwa gwajin golayen su.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG