Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Kama Ali Tera Ya Janyo Muhawara a Nijer


Mahamadou Issifu Shugaban Kasar Nijar

Wani jirgin saman kamfanin Ethiopia da ya sauka birnin Yamai a yammacin jiya ne ya zo da Ali Tera hannuwansa daure da ankwa kuma nan take jami’an tsaro suka fice da shi zuwa ofishin hukumar ‘yan sandan farin kaya.

Alkali mai tuhuma Procureur de la Republique, Chaibou Samna ya gayawa Muryar Amurka cewa Ali tera na fuskantar wasu tarin zarge zarge da suka hada da tunzura jama’a don gudanar da taron tayar da bore dauke da makamai da nufin bijirewa hukuma, da yunkurin tada zaune tsaye da kuma neman haddasa fitina a tsakanin ‘yan kasa, da kuma barazanar kisan kai.

Wannan dan tiliki da ya shafe shekaru sama da 20 a kasar Amurka ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin shugaba Issouhou Mahamadou ta hanyar sakwannin da yake aikawa a shafukan sada zumunta.

A ra’ayin Adamou Manzo na jam’iyar PNDS Tarayya, halin da Ali Tera ya tsinci kansa ciki a yau ya isa abin ishara.

Sai dai a na su bangaren magoya bayan jam’iyar MODEN Lumana irin su Bana Ibrahim na ganin matakin hukumomin na Nijer tamkar keta hakkin dan adam ne.

Bayan ya shafe daren jiya laraba a ofishin hukumar ‘yan sandan PJ, Ali Tera ya bakunci gidan yarin Filingue dake da nisan km sama da 170.

Kafin a tuso keyar sa zuwa Nijer, Ali Tera ya shafe makwanni a wani gidan yarin Amurka inda aka tsare shi sakamakon rashin mallakar takardun izinin zama a wannan kasa.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG