Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Gwamnonin Arewa Sun Gudanar da Taronsu a Bauchi


Taron Matan gwamnonin arewa
Taron Matan gwamnonin arewa

A taron nasu, matan gwamnonin arewa sun cimma matsaya kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da matsalar shan miyagun kwayoyi da ilmin ‘ya mace tare da alkawarin mara wa mazajensu baya

Matan gwamnonin arewa sun yi taronsu na biyar a garin Bauchi inda matar gwamnan Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar, ta zama shugabar kungiyar.

Taron ya tattauna kan wasu abubuwa dake da mahimmanci. Wadannan ko sun hada da batun shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi, ilmin ‘ya’ya mata, goyon bayan shirin matar shugaban kasa da marawa mazajensu baya domin su yi nasara a ayyukansu.

A jawabinta, sabuwar shugabar kungiyar Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar, ta jaddada goyon bayansu ga duka shirye-shiryen da zasu kawo ci gaba, musamman ma ga mata.

Ita ma matar gwamnan jihar Gombe, Hajiya Adama Ibrahim Dankwambo, ta yi karin haske akan muhimman abubuwan da suka tsayar a taron, inda ta nuna cewa kowa ya san illar da miyagun kwayoyi ke yiwa matasa da matan aure.

A sakonsa ga taron gwamnan Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya bukaci ganin matan sun baiwa mazajensu goyon baya bisa ga duk ayyukan da zasu yi nan gaba.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG