Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nijar Kan Haramta Sa Nikabi a Kasashen ECOWAS


Wasu Shugabannin Kasashen Shugaba

Kasashen Afirka ta Yamma na Ecowas sun yanke hukuncin haramtawa ko wace mace amfani da Nikabin da ke boye fuskarsu baya ga idonsu da shi kadai zaka iya gani. wasu mata a Nijar suna ganin ya dace wasu kuma sun ce sam wannan bai dace ba.

Bincike ya nuna cewa kaso 99 daga cikin 100 na ‘yan Jamhuriyar Nijar Musulmi ne, wanda wannan ce tasa wasunsu suka tofa albarkacin bakinsu game da sabon hukuncin da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da aka fi sani da Ecowas.

Wanda suka taru suka yanke dokar haramtawa mata sanya nikabi da ke rufe musu fuskarsu baka ganin komai a jikinsu sai idanuwansu. Wanda suna ganin a yadda matsalar tsaro take a kasashen to dole a dauki wannan mataki.

Wata ta bayyana mana yadda suke kallon abin da cewa ba laifi bane in dai har za ayi haka ne don kiyaye lafiya da rayukan al’umma ne. inda wata kuma a nata jawabi tace ai Nijar ba kamar sauran kasashen da suka yanke hukuncin ba ce.

Musamman in suka yi la’akari da cewa wasu kasashen da dama daga cikinsu bas u da yawan musulmin da Nijar ke dashi, amma su wannan doka a kasarsu ai tamkar tauye musu hakkinsu ne da ya kamata su samu na addini.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG