Ganin an katse masu hanyar shiga yanar gizo, matasa a kasar Cuba, cikin sirri, sun hada dubban komfutoci da wata boyayyiyar hanyar sadarwa mai tsawon mil da dama a fadin birnin Havanah, waddda ta ba su damar zantawa da abokai, da wasannin bidiyo, da kuma kwafar fina-finan bidiyo, ta wannan hanyar da akasarin mutane ba su iya shiga.
An hana mutanen Cuba shiga yanar gizo daga gidajensu, in banda wasu kalilan. Idan mutum na son shiga duniyar gizo to sai dai kaje inda gwamnatin ta ware kabiya kudi mai yawa.
Matasan dai sunyi amfani da hazakarsu wajen hada kayayyakin da basu da tsada da wahalar samu, wajen kirkirar wannan hanyar sadarwar, batare da taimakon wata gwamnati ko kungiya a duk fadin duniya ba.
A yanzu haka matasan kasar na walwalarsu akan yanar gizo inda suke sada zumunci da sauran mutane dake fadin duniya, yin wasanni na bidiyo, aika sakonnin rubuto da hotuna dadai sauransu.
A tabakin wani matashi dan shekaru ashirin da biyu, yace, “tabbas muna bukatar hanyar dazamu samu shiga cikin yanar gizo, saboda akwai abubuwan amfani masu dinbin yawa a cikin yanar gizo, a kalla ma mutum zaiji dadi ganin cewar kana da hanyar da zaka hadu kayi mu’amula da dinbin mutane, ta inda zakuyi magana harma da sauye-sauyen wasu abubuwa masu amafani.”
Kasar Amurka dai na kokarin hada sabuwar dangantaka da kasar ta Cuba, don ganin an taimakawa da kasar wajen samar da kayan fasaha irin na Amurka.