Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Mata Da Maza a Jihar Neja Sun Koyi Sana'oin Hannu


Matasa mata da maza sun koyi sana'a.

Matasa maza da Mata sun koyi sana'oin hannu a jahar Naijan Nageriya.

An gudanar da wani gagarumin biki a jahar Naijan Najeriya inad aka yaye wasu matasa maza da mata da yawan su ya kai 2000 da suka koyi sana'oin hannu daban daban a jahar Naija kuma gwamnatin tace ta kashe kudi sama da miliyan dari shidda da tamanin wajan horar da wadan nan matasa da kuma sama masu aikin yi domin su fara dogaro da kansu.

Alhaji Hasan Nuhu shine babban darektan kula da wannan shiri a jahar Naija kuma yayi tsokacin dalilin yin hakan a manufar su ta mataki na farko wato samar wa da matasa aikin yi na biyu kuma yakar talauci na uku kuma samar da tsaro da natsuwa a kasa.

Malama Amina Aliyu na daya daga cikin masu koyar da matasan inda ta fadi cewar suna bin matasan har cikin karkara ne su koyar da su amma tace sun fuskanci matsaloli da dama, tayi karin bayanin cewar a cikin matsalolin da suka fuskannta sun hada da rashin jin harsunan wasu, wasu kuma sun dauki lokaci kafin su fahimta da abin da ake koya masu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00

XS
SM
MD
LG