Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Addu'oin matasa a Nijar domin ceto kasar daga matsalolin tsaro da na zamantakewa.

A harabar babban masallacin juma'ar kofar fadar Katsinan Maradi ne kungiyar matasan kasar ta Nijar suka yi taron addu'oi da na neman zaman lafiya a cikin kasar baki daya, Malam Ibrahim Mainasara Danjuma shine babban sakataren kungiyar ta matasa kuma yayi karin bayani cewar.

"Mun kafa wannan kungiyar ne domin tallafawa kasar mu a matsayin matasa domin mun lura cewa kasar mu na bukatar addu'a domin muna cikin mawuyacin hali, shine makasudin wannan taro kuma mun gayyaci manyan malamai da dukkan wandanda Allah yaba damar halattar taron domin abin ya shafi kowa musamman tawajan faduwar tattalin arzikin kasa"r.

Manyan limamai sun halacci wannan taro kuma sunyi addu'oi da dama, matasa ma ba a barsu a baya ba kuma da yawansu sun tofa albarkacin bakinsu musamman akan muhimmancin taron wand gwamnan jahar Malam Abdu Muhamma ya jagoranta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00

XS
SM
MD
LG