Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Maganin Rigakafin Cutar Cizon Sauro


Sauro wanda yake haddasa cutar zazzabin Malaria
Sauro wanda yake haddasa cutar zazzabin Malaria

Kididdigar da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO ta fitar akan maganin rigakafin cutar cizon sauro ya kawo rudani da rashin fahimta saboda an dauka duk magungunan karfinsu na warkar da cutar ya ragu.

Kididdigar da Hukumar Kiwon Lafiya ta fitar ya zo ne a daidai lokacin da masu kamuwa da cutar cizon sauro a Najeriya da ma wasu kasashen ke kokawa da rashin ingancin magungunan da suke sha.

Ahmed Ibrahim Yakasai shugaban kungiyar masu hada magunguna ta Najeriya ya yi karin haske dangane da korafin rashin ingancin magungunan cutar cizon sauro. Ya ce binciken da kasar Amurka ta yi akan maganin rigakafin cutar cizon sauro ne kuma akan kashi goma na cikin magungunan ta yi. Ya ke cewa sau da yawa idan mutane suka ji an bayar da sakamakon bincike sai su dauka duka magungunan ne ya shafa. Ya ce haka duk binciken da a keyi a Najerya akan maganin rigakafi ne.

Binciken hukumar kiwon lafiya ta duniya akan daya cikin goma ne inji Yakasai. Amma duk da haka ba za a ce babu jabun magunguna ba.

Wani Husseni Muhammad wanda ya farfado daga cutar malaria, ya ce ya sha magununan da dama. A cewarsa akwai wadanda mutum zai sha ya samu sauki amma kuma cutar ta sake dawowa kuma haka ciwon zai ta kaiwa ya dawo har a samu a warke.

A can baya gwamnati da masu kiyaye ingancin magunguna sun fito da wani tsari na baiwa duk wani magani lambar waya inda mai sayen maganin zai aika da sakon kar ta kwana domin tabbatar da ingancin maganin.

A Najeriya da wasu kasashe masu tasowa, miliyoyin yara da manya ne suke mutuwa kowace shekara sanadiyar cutar cizon sauro, cutar da za a iya maganceta ba sai ta kai ga daukan rai ba.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG