Accessibility links

Jam'iyyar PDM ko kuma sabuwar jam'iyyar PDP ta yi furuci game da tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya

Mai magana da yawun sabuwar jam'iyyar PDP ya ce shugabannin Najeriya su ne suke raba kawunan mutane domin su cigaba da mulkin kasar yadda suka ga dama. Matsalar Najeriya bata ban bancin addini ba ne haka kuma bata ban bancin kabila ba ne.

Abun da ya damu 'yan Najeriya shugabannin mara sa adalci, shugabanni azzalumai, barayi da mara sa gaskiya. Abun da ya fi kyau shi ne duk kabilan Najeriya da bangarori daban daban su hada kai a kawar da azzaluman shugabannin. Ya ce abun da sabuwar PDP zata yi ke nan.

Jam'iyyar PDM jam'iyya ce da ta gaji yin gwagwarmaya. Marigayi Shehu 'YarAdu'a da ya kafa jam'iyyar ya yi ne domin ya yaki zalunci. Shi kansa ba matalauci ba ne amma a kan gwagwarmayar ya rasa ransa. Don haka su a jam'iyyar basa tsoron gwagwarmaya kuma sai sun ga bayan duk azzaluman shugaban PDP wadanda halayansu suka haddasa rashin tsaro a kasar.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG