Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar 'Yan Damfarar 419 a Najeriya


Duk da kokarin da hukumomi a Najeriya da Amurka ke yi na kame da kuma dakile ayyukan 'yan danfarar kudin Banki da aka fi sani da 419 ko yahoo Yahoo a Najeriya, har yanzu wasu 'yan Najeriya, musanman matasa, na ci gaba da gudanar da wannan muguwar sana'ar ta hanyoyi da dama.

Wasu daga cikin hanyoyin dai sun hada da kiran wayar mutun tare da shaida masa cewar daga bankin da yake ajiya ake kiransa, wato customer care, - alhali kuwa 'yan danfara ne. Sau da yawa dai sukan aiko da wasu lambobi da suke neman ka gaya masu lambobin, da zarar mutum ya fada tarkonsu, sai su wawure kudaden ajiyar mutane ba tare da bata wani lokaci ba.

Sau da yawa dai sukan bugo wayar ne bayan an tashi aiki ranar Juma'a zuwa Asabar da Lahadi, wato ranakun da suka san bankuna basa aiki, balle wanda aka danfara ya garzaya banki domin neman ceto.

Ko wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin ya taba fuskantar irin wadannan 'yan danfarar da suka buga ma shi waya har sau 23 duk kuwa da cewa wayarsa ta nuna 'yan danfara ne.

Ko a watan Satumba sai da jami'an hukumar FBI suka kama wasu 'yan asalin Najeriya dake zaune a Amurka da suka danfari wasu 'yan Amurka fiye da 100 dala miliyan 117.

Saurari rahoton Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:58 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG