Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawaki Davido Ya Gwada Ficensa Inda Fittatun Mutane Suka Tura Masa Sama Da Naira Miliyan 100


Davido (Hoto: Davido Instagram Courtesy - Fortune)

An yi ta cece- kuce a kafafen yanar gizo tun bayan da Fitattacen mawaki a Najeriya David Adeleke da aka fi sani da Davido ya wallafa cewa yana bukatar abokansa su hada masa kudi har Naira Miliyan 100 don bikin ranar haihuwarsa da ke tafe a ranar 21 ga watan Nuwamba.

To sai dai wani abin mamaki shi ne yanda cikin sa’o'i kasa da 24, ya sami sama da miliyan 100 a asusunsa na ajiyar kudi na banki, lamarin da ya sa ya kara adadin zuwa Miliyan 200.

Wannan dai ba shi karon farko da mawaka ko fittatun mutane ke sanya gasa tsakanin matasa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ba, don a nishadantar ko a fadakar koma a ilimatar da a'umma, sai dai a wannan karon mawaki Davido ya ta da cece-cuce a kafafen, duba da yadda cikin kankanin lokacin a ka hada masa makudan kudade.

Davido, wanda ke da mabiya sama da miliyan 30 a Instagram da Twitter, ya fara gasar ne ta hanyar wallafa wani rubuta a kan shafinsa na kafar Instagram da cewa, ya kasance yana tallafawa wasu, a yanzu kuma lokaci ne da su ma za su mai da martani.

Daga cikin mutane da su ka shiga wannan gasa na tura kudi ga mawakin har da attajirin dan kasuwan nan Femi Otedola da sarkin Elegushi da ke jihar Legas da mawaka irin su Don Jazzy, Uji Maestro, Pasuma, Larry Gaaga, Patoranking, Zlatan da kuma MC Galaxy da dai sauransu

Wannan lamari ya sanya mutane da dama kira ga abokansu da su yi musu irin na mawaki Davido.

XS
SM
MD
LG