Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Na Neman Dalar Amurka Miliyan 434 Domin Taimakawa Kabilar Rohingya


'Yan kabilar Rohingya da suke arcewa daga Mynmar saboda kisan kiyashi da ake yi masu suna ketarewa zuwa kasar Bangladesh

Shugabannin cibiyoyin samarda agaji na Majalisar Dinkin Duniya, MDD sun yi wani taro na kwana guda domin neman tallafin Dala Miliyan $434.

Shugabannin cibiyoyin samarda agaji na Majalisar Dinkin Duniya, MDD sun yi wani taro na kwana guda domin neman tallafin Dala Miliyan $434 domin tallafawa mutane Miliyan 1.2 ciki har da ‘yan gudun hijirar Rohingya da masu taimaka musu a kasar Bangladesh.

Kafin a gudanar da taron bude asusun, wani kakakin daya daga cikin cibiyoyin bayar da agaji ta MDD ya ce yanzu yawan ‘yan Rohingya da suka yi gudun hijira domin gujewa tashin hankali da muzugunawar da ake musu a Myanmar cikin watanni biyun da suka gabata sun kai dubu 600.

Hukumomin agaji sun yi imanin cewa tashin hankalin dake samun mafi karancin tallafi a duniya, wanda hakan yasa madugun Hukumar kula da aiyukkan bada agaji na MDD, Mark Lowcock, yake gayawa mahalarta wannan taron wuni guda cewa ana kokarin hada hancin kudade ne don a ceto rayukan ‘yan gudun hijirar kuma a kare su daga fuk wata kuntatawa a gaba.

Dubban ‘yan gudun hijira sun fara dunguma birnin Cox’s Bazar na Bangladesh ne daga ranar 25 ga watan Agusta bayan da wasu tsagerun Rohingya suka kashe ‘yan sandan kasar Myanmar tara, wanda ya haddasa rikicin.

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG