WASHINGTON, DC —
Dan wasan tsakiya na Barcelona, Xavi, yace yana fata Neymar ba zai bari kararrakin da aka shigar game da komawarsa FC Barcelona da kuma wasu matsalolin su kawar masa da hankali daga taka tamaula yadda ya kamata ba.
Santos ta Brazil, inda Neymar ya fito, ta kai karar mahaifinsa da wasunsu, duk dangane da komawarsa Barcelona a kan kudi Euro miliyan 40.
Masana tamaula a can gefe kuma, sun fara nuna shakkun ko manajan Arsenal, Arsene Wenger, zai iya kai ta zuwa ga wasan karshe na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai, domin duk lokacin da aka shiga wasan kwaf daya, ana yin waje-rod da kungiyar.
Wenger yace sau biyu a can baya Arsenal tana karawa da FC Barcelona, sau biyu da Bayern Munich, kungiyoyin da babu kanwar lasa a cikinsu. Amma masu fashin bakin suka ce, laifin na Arsenal ne domin ba ta tabuka wani abu a zagayen farko, ta yadda idan aka shigo zagaye na biyu na kwaf daya, zata kaucewa haduwa da irin wadannan manyan kulob dake doke ta.