Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Micheal Flynn Ya Ci Amanar Kasa-Alkali Sullivan


Micheal Flynn da lauyoyinsa a gaban alkali

Wani Alkali a Washington DC ya nuna rashin jin dadinsa ainun ga mai baiwa shugaban kasa Donald Trump shawara kan harkokin tsaro na farko, Michael Flynn, kan karyar da ya yiwa masu bincike akan maganar da yayi da Rasha ‘yan makonni kafin Trump ya hau mulki, amma kuma ya jinkirta yanke masa hukunci.

Alkalin kotun tarayya na Gunduma, Emmet Sullivan, ya ce ba zai iya boye rashin jin dadinsa da damuwarsa ba kan abin da Flynn ya yi, kafin daga baya ya amince da bukatar lauyoyin Flynn na soke zaman yanke hukuncin.

Flynn ya tabbatarwa Alkali Sullivan cewa, ya sani ba karamin laifi bane ayi wa masu bincike ‘karya, lokacin da suka tambayeshi zantawarsu da jakadan Rasha na wancan lokacin a Amurka, Sergey Kislyak.

Alkalin ya fadawa Flynn cewa abin da ya aikata babban laifi ne, kuma cin amanar ‘kasa ne.

Mai bincike na musamman Robert Mueller ya bayar da shawara kan ‘dan shekaru 60 a duniya, Flynn, kuma tsohon janar na soja wanda a baya ya taba zama shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Soja, da kada a yanke masa hukuncin da zai kaishi ga gidan yari, saboda irin hadin kan da yake baiwa binciken da yake gudanarwa kan alakar kwamitin kamfen din Trump da Rasha, da kuma ko Trump ya karya doka a yunkurin dakatar da biciken da ake yi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG