Mijin shahararriyar mawakiyar salon wakar country Dolly Parton, Carl Thomas Dean, ya mutu yana da shekaru 82.
Parton ce ta yada labarin mutuwar a sanarwar data wallafa a shafukanta na sada zumunta a jiya Litinin.
"Ni da Carl mun shafe dimbin shekaru masu dadi a tare," kamar yadda ta wallafa. "kalamai ba za su yi adalci ba wajen bayyana irin kaunar da ke tsakaninmu tsawon fiye da shekaru 60. Ina godiya game da addu'o'i da alhininku."
Ma'uratan sun yi aure a 1966 kuma basu haihu ba.
Ba'a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, duk da cewarsakon da ta wallafa ya bayyana cewa ya mutu ne a garin Nashville na jihar Tennessee, inda ma'uratan ke zaune.
A cewar sakon da Dolly Parton ta wallafa a shafinta na sada zumunta a jiya Litinin, za'a birne Dean a wani kebebban bikin da danginsa na kusa zasu halarta.
Dandalin Mu Tattauna