Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Pence Ya Ce Ya Kamata A Sake Yarjejeniyar da Aka Cimma da Iran


Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence, da Shugaban Israila Reuven Rivlin yayinda suke ganawa a fadar shugaban dake birnin Qudus yau, Janairu. 23, 2018.
Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence, da Shugaban Israila Reuven Rivlin yayinda suke ganawa a fadar shugaban dake birnin Qudus yau, Janairu. 23, 2018.

Yau a birnin Qudus, yayinda yake ci gaba da ziyarsa a Gabas ta Tsakiya, Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, ya sake nanata aniyar gwamnatinsu na neman sauya yarjejeniyar da aka cimma da Iran akan shirin nukiliyarta

A yau Talata, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya nanata aniyar gwamnatinsu, cewa ya kamata, a sauya yarjejeniyar da aka cimma da Iran kan shirinta na makamin nukiliya, sannan ya ce, shirin mayar da ofishin jakadancin Amurka da ke Isra’ila zuwa Birnin Kudus, alama ce da ke nuna himmatuwar da Amurka ta yi wajen cimma wannan buri.

Yayin da yake ganawa da Shugaban Isra’ila Reuven Rivlin, Pence ya ce, Amurka na aikawa kawayenta da ke nahiyar turai sako ne, kan bukatar su sauya matsayar da aka cimma a shekarar 2015, wacce ta samar wa Iran sassauci kan takunkumin da aka kakabata mata, da wajewar cewa za ta takaita shirinta na mallakar makamashin nukiliya, domin kada ta kai ga mallakar fasahar nukiliya.

Shugaban Amurka Donald Trump da shugabannin Isra’ila, sun nuna adawarsu kan wannan yarjejeniya, suna masu cewa Iran ta fi cin riba a wannan yarjejeniya.

Ita dai kungiyar tarayyar Turai, ta bayyana matsayarta kan cewa, samar da kasashe biyu, shi ne mafita ga rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Falasdinu, tare da barin Kudus a matsayin babban Birnin kasashen biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG