Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane sun ji Dadin Tsawaita Tsagaita Bude Wuta


Shugaban Hamas
Shugaban Hamas

Miliyoyin mutane a Zirin Gaza da Kudancin Isira'ila, sun ji dadin tsawaita tsagaita bude wutar da aka yi tsakanin Isira'ila da Hamas.

Masu shiga tsakani a Masar sun yi nasarar tsawaita tsagaita bude wutar na tsawon kwanaki 5 don a samu karin lokacin tattaunawar da ake yi a birnin Alkhahira da zummar cimma kwakkwarar yarjajjeniya ta kawo karshen yaki a Gaza.

Tsawaitawar ta fara aiki ne daga tsakar daren ranar Laraba, kuma ta kankama duk kuwa da wata 'yar musayar rokoki da hare-haren jiragen sama. Ba a samu rahoton jin rauni ba.

A birnin Tel Aviv dubban mutane sun taru a jiya Alhamis su ka bukaci gwamnatin Isira'ila da hukumar sojin kasar da su kawo karshen rokokin da Falasdinawa ke cillowa zuwa Isira'ila.

Falasdinawa wajen 1,950 sun mutu a Zirin Gaza a wannan yakin, akasarinsu fararen hula ne a cewar Majalisar dinkin duniya, da jami'an Falasdinu. Isira'ilawa kuma 67 ne su ka mutu, kuma kusan rabinsu sojoji ne.

XS
SM
MD
LG