Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Minista Ocholi Ya Rigamu Gidan Gaskiya


Minista James Ocholi,wanda Allah Ya yiwa rasuwa ranar Lahadi nan.

Ministan ya rasa ransa ne tare da dansa lokacin da motarsu tayi hadari kan hanyar Abuja zuwa kaduna.

Karamin ministan ayyuka na Najeriya Mr.James Ocholi ya rasa ran sa a sakamakon hatsarin mota kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Baya ga ministan da dan sa da su ka rasu nan take,matar ministan da ta samu munanan raunuka ma ta rasu daga bisani

Ganau ga wannan hatsarin Aliyu Ahmad na Jaridar Rariya, ya ce tayar motar ministan ta gaba ce ta fashe inda motar ta yi alkafura sau da dama da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ministan nan take.

Hatsarin ya auku ne kimanin kilomita 40 daga Kaduna kan hanyar Abuja daf da wani kauye da a ke cewa Doka.

Ganau din ya ce motar ministan ce ita kadai ta samu hatsarin inda jami’an tsaro da ke yiwa ministan rakiya a wata mota daban su ka fara kawo dauki don kai gawar asibitin wannan kauye na Doka da kuma kula da direban ministan wanda ya samu raunuka.

Karamin ministan kwadagon dai daga jihar Kogi na da cikin ministocin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada bayan share wata biyar kan mulki.

Ocholi wanda babban lauyan Najeriya ne “SAN” ya rasu ne ya na mai shekaru 55.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

--

XS
SM
MD
LG