Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Ministan Harkokin Wajen Lebanon Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa


Ministan harkokin waken Lebanon Nassif Hitti da ya yi murabus
Ministan harkokin waken Lebanon Nassif Hitti da ya yi murabus

Ministan harkokin wajen kasar Lebanon Nassif Hitti ya mika takardar ajiye aikinsa watanni bayan da aka ba shi mukamin.

Kafin mika takardar tasa ya yi gargadi kan yadda komadar tattalin arziki da Lebanon ke fuskanta da rashin mayar da hankali wajen shawo kan wannan matsala, ka iya zama babbar barazanar da kasar ba ta taba gani ba tun bayan yakin basasan da aka yi.

A cikin wata sanarwa da Hitti ya fitar ya ce, "na lura cewa akwai ubanni gida da dama a kasata wadanda ke da ra’ayoyi masu karo da juna. Muddin ba su hada kansu don su ceci al’umar Lebanon ba, ba fata nake yi ba, kowa da kowa zai shiga uku."

Frai ministan Lebanon (hagu) a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Lebanon (dama)
Frai ministan Lebanon (hagu) a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Lebanon (dama)

Hitti ya kara da cewa, Lebanon na cikin hadarin zama "kasar da za ta zamanto komai ba ya aiki."

Babban jami'in diflomasiyyan ya zama ministan harkokin waje ne a watan Janairu a gwamnatin ta Firayim Minista Hassan Diab.

Rahotanin sun nuna cewar Hitti ya shiga yanayi na takaici ne sanadiyyar sukar da Diab ya yi ga Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian, yayin wata ziyara da jami’in diplomasiyyan na Faransa ya kai Beirut a kwanan nan.

Sa'o'i kadan bayan Hitti ya ajiye aiki, shugaba Michel Aoun ya nada Charbel Wehbe a matsayin sabon ministan harkokin kasashen waje kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG