Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Faransa Ya Kai Ziyarar Jaje Nijar Saboda Harin 'Yan Boko Haram


Laurent Fabius, Ministan Harkokin Wajen Faransa
Laurent Fabius, Ministan Harkokin Wajen Faransa

Bayan ya kai ziyara kasashen Chadi da Kamaru ministan ya karkata zuwa Nijar saboda yiwa kasar jaje da kuma jinjina mata akan yadda ta tukari 'yan kungiyar Boko Haram

Ministan yace ya zo kasar Nijar da batutuwa guda hudu.

Yace 'yan Boko Haram manya manyan 'yan ta'ada ne. Ya kira Najeriya ta sa kaimi domin ta yakesu. Yakin da kasashen Chadi, Kamaru da Nijar keyi da 'yan Boko Haram abu ne na a jinjina masu. Yace kasar Faransa na kan gaba domin jinjinawa kasar Nijar domin irin fafitikar da ta keyi wajen kakkabe 'yan Boko Haram.

Ministan Mr. Fabius yace tarayyar Turai na kan gaba kuma da burin saka hannu domin a yaki 'yan Boko Haram.

Dangane da ziyarar ministan daga Faransa wasu 'yan kasar ta Nijar sun bayyana ra'ayoyinsu. Sun ce suna goyon bayan ziyarar iadan kuma abun da ya zo dashi na alheri ne Alla ya tabbatar. Dama mai kaunar mutum shi ne yake jajintawa idan abun bakin ciki ya faru ko kuma taya murna idan abun farin ciki ne.

Ga rahoton Shuaibu Manni

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG