Malam Adamu Adamu da shugaban jami’ar tarraya dake Oye Ekiti, Prof. Kayode Shoyemekun ya wakilta yayi kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ministan a wani taro a Oye Ekiti. Malam Adamu ya ce don samar da ingantacen ilimi da kuma kwarewa yana kira ga jami’o'in kasar da samar da dalibai suke da kwarewa da basira da kwazo.
A nasa jawabin sakataren hukumar dake kula da jam’ioin Nigeria, NUC a takaice, Prof Rashid Abubakar wanda daraktan hukumar Dr. Chris Maiyaki ya wakilta ya ce suna daukan matakai kan jami’oin gwamnati da masu zaman kansu a Nigeria domin tabbatar suna bada ilimi mai inganci da nagarta.
Sakataren NUC Rashid Abubakar ya shawarci iyaye da su yi hulda da jami’oin da hukumar NUC ta tanttance a fadin Nigeria. A nasa bangaren shugabn taron mai mukamin sarautar gargajiya ta Oni of Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya bukaci daliban Nigeria da su rungumi tarbiya mai kyau wajen gina kasa.