Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaron Amurka Jim Mattis Ya Caccaki Rasha


Ministan Tsaron Amurka Jim Mattis
Ministan Tsaron Amurka Jim Mattis

Yayinda kasashen duniya ke cigaba da korar 'yan diflomasiyar Rasha akan harin guba da ake zargin Rasha da yi, minisatan tsaron Amurka Jim Mattis ya caccaki kasar ta Rasha akan lamarin.

Ministan tsaro na Amurka Jim Mattis ya caccaki Rasha, saboda matakai masu hadari da gangan ci data nuna, yana mai cewa, "abune tabbatacce" cewa hukumomin Rasha a Moscow, sune suka kai hari da makaman guba kan wani tsohon dan leken asirin Rasha shi da 'yarsa a Britaniya.

Jim Mattis,ya furta haka ne lokacind yake magana da manema labarai jiya Talata a ma'aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon, lokacinda suka nemi jin ta bakinsa kan lamarin da ya janyo rikicin difilomasiyya da bai yiwa Rasha dadi ba.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta fada jiya Talata cewa, fiyeda kasashe 25 ne suka kori 'yan leken asirin Rasha 150, wadanda suke fakewa da rigar difilomasiyya. Hukumomin Amurka dake nan Washington, sun bayyana fatar za'a sami karin kasashe da zasu bi sawun Amurka kan wannan mataki.

Tunda farko a jiya Talata, kungiyar tsaro ta NATO ta bada sanarwar ta kori jami'an difilomasiyyan Rasha bakwai, kuma ta hana wasu uku takardun fara aiki, a zaman wani shiri mai karfi daga kasashen duniya kan zargin da suke yiwa Rasha.

Rasha dai ta musanta zargin tana da hanu a harin da aka kai da makamai masu guba. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, yace Rasha zata maida martani nan da mako daya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG