Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen NATO Zasu Karfafa Tsaro a Iyakar Kasar Turkiya


Sakataren NATO Janar Jens Stoltenberg

Mako guda bayan da Turkiya ta kakkabo jirgin yakin Rasha a iyakarta da Syria, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Tsaro ta NATO, na duba yadda za a kara tsaurara matakan tsaro a iyakar kasar ta Turkiyya.

Jami’ai a taron da ministocin suka gudanar a Brussel a jiya Talata, sun ce daga cikin matakan da ake dubawa, har da batun tura karin jiragen ruwan yaki a tekun Meditareniya da jiragen sama na yaki a filin jirage da ke Incirlik, da kuma bunkasa makamai masu linzami.

Har ila yau ministocin sun kwatanta abinda ke faruwa a iyakar Turkiyya da Syria, a matsayin wani lamari mara tabbas, suna masu jaddada za su ci gaba da samar da matakan kariya ga duk wata kasa da ta kasance mamba a kungiyar ta NATO.

Sakatare Janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce duk mambobin kungiyar su yi shawara nan da ‘yan makwanni masu zuwa game da irin taimakon da za su baiwa Turkiyya

Ministan harkokin wajen Lithuania, Linas Linkevicius, ya ce, ya kamata a baiwa Turkiyya duk irin taimakon da ta nema, yana mai karfafa cewa duk wani abu da ke barazana ga kasa daya, yana baraza ne ga kungiyar ta NATO.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG