Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mitt Romney Ya Fara Yakin Neman Zabe


Mitt Romney ad mataimakinsa Paul Ryan kan dandali a zauren babban taron jam'iyyar Republican

Mitt Romney da mataimakinsa Paul Ryan zasu yi yakin neman zabe a Florida da Virginia da Ohio a bayan da suka amshi kambin takara na Republican

A yau jumma’a dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Republican a nan Amurka, Mitt Romney, yake fara kyamfe nasa na neman wannan kujera a bayan babban taron jam’iyyar, inda zai yi gangami a wasu jihohin da zasu kasance masu muhimmanci a karawar da zai yi da shugaba Barack Obama a watan Nuwamba.

Mr. Romney, tare da zabinsa na mataimakin shugaban kasa Paul Ryan, zasu yi gangami a jihohin Florida da Virginia da kuma Ohio. A daren jiya alhamis dan takarar ya amshi kambin tsayawa takara da jam’iyyar ta ba shi, inda yayi alkawarin maido da kimar Amurka.

Mr. Romney ya fadawa babban taron jam’iyyar ta Republican a garin Tampa dake Jihar Florida cewa ya so a ce shugaba Obama ya samu nasara a shekaru hudun da yayi a kan wannan kujera. Amma kuma yace alkawuran da shugaban yayi sun ja gefe, suka kawo rashin gamsuwa da rarrabuwa, yana mai fadin cewa Amurkawa sun cancanci abinda ya fi haka.
A cewar Mr. Romney, "wannan shugaba yana iya fada mana cewa laifin wani ne (ba nasa ba). Wannan shugaba yana iya fada mana cewa zai gyara kura-kuransa a cikin shekaru hudu masu zuwa. Amma kuma wannan shugaba ba zai iya fada mana cewa halin da Amurkawa suke ciki ya fi kyawun na lokacin da ya hau kan mulki ba."
XS
SM
MD
LG