Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mohammed Morsi ya lashe zaben fidda gwani a Masar


Siyasar Masar

Hukumar zaben Masar ta ayyana dan takarar kungiyar Muslim Brotherhood a zaman wanda ya lashe zaben fidda gwani da aka yi tsakaninsa da tsohon Prime Ministan Ahmed Shafiq.

Hukumar zaben Masar ta ayyana dan takarar kungiyar Muslim Brotherhood a zaman wanda ya lashe zaben fidda gwani da aka yi tsakaninsa da tsohon Prime Ministan Ahmed Shafiq.

Ana bada wannan sanarwar magoya bayan Morsi suka buge da murna a dandalin Tahrir. Morsi ya kada tsoho Prime Minista Ahmed Shafiq.

Dama ranar Alhamis ya kamata a baiyana sakamako zaben, amma hukumar zaben kasar tace tana bukatar karin lokaci domin ta bincike zarge zargen magidu zabe da dukkan yan takarar suka yi.

Tunda farko jami’an kasar Masar sun girka karin jami’an tsaro a titunan birnin Alkahira da kuma a muhimman wurare kafin a bada sanarwar sakamakon zaben da aka shirya gabatarwa da misalin karfe uku na yamma agogon Masar.

Magoya bayan yan takarar biyu sunyi barazanar yin zanga zanga idan dan takarasu ne bai samu nasara ba. Jiya asabar da dare ma dubban yan Masar ne suka gangami a tsakiar birnin Alkahira cikin tsauraran matakan tsaro domin nuna goyon bayansu ga yan takarar guda biyu.

XS
SM
MD
LG