Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mueller Zai Ba Da Shaidar Da Za Ta Kai Ga Tsige Trump - Nadler


Sai dai duk da haka, ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republikan ta Trump, sun yi hasashen cewa ba za’a samu wasu bayanan da suka wuce wadanda aka ji a baya ba.

Wani jigo a jam’iyyar Dimokrat a majalisar wakilai ya ce mai bincike na musamman Robert Mueller zai ba da muhimmiyar shaida da za ta ba da damar a kai ga tsige shugaba Amurka Donald Trump.

"Wannan wani shugaban kasa ne da ya karya doka ta hanyoyi shida daga ranar lahadi,” inji shugaban kwamitin da ke kula fannin shari’a na majalisar wakilai, Jerold Nadler, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Fox a jiya Lahadi.

Sai dai duk da haka, ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republikan ta Trump, sun yi hasashen cewa ba za’a samu wasu bayanan da suka wuce wadanda aka ji a baya ba.

Shi ma a lokacin da yake tattunawa da gidan talabijin na Fox a jiya lahadi, dan majalisa Doug Collins, wanda shi ne babban dan jam’iyyar Republikan a kwamitin shari’ar, ya zargi ‘yan jam’iyyar Demokrat da sake komawa kan batutuwan da aka riga aka sani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG