Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimman Labaran Da Suka Faru a Karshen Mako a Fannin Nishadin Najeriya


Umar M. Shareef (Hoto: Umar M. Shareef Instagram)
Umar M. Shareef (Hoto: Umar M. Shareef Instagram)

Dan Uwan Rahama Abba Ya Angwance

Dan uwan jaruma Rahama Sadau, Haruna Sadau, wanda aka fi sani da Abba, ya angwance da amaryarsa Zainab a karshen makon da ya gabata. Tun gabanin auren an ga Rahama tana ta saka hotunan Abba tana mai taya shi murna, bisa wannan abin alheri da ya same shi. “Ina mai addu’ar wannan aure zai zama mai cike da nishadi ga duka ku biyu.” Rahama ta rubuta a shafinta na Instagram dauke da hotan Abba da amaryarsa Zainab.

Abba da Amaryarsa Zainab (Hoto Rahama Sadau Instagram)
Abba da Amaryarsa Zainab (Hoto Rahama Sadau Instagram)

Sabuwar Wakar Umar M. Shareef

Fitaccen mawaki kuma jarumi a Kannywood, Umar M. Shareef, ya saki sabuwar waka mai suna “Wa za na ba kaina,” wacce ya yi tare da Maryam wacce aka fi Sani da "Maryam Bodyguard."

“Ko ba ki zo ba ai kina nan....

"A zuciya ki ke raka ni.” Wasu daga cikin baitukan wakar suke cewa a cikin wakar.

Tsohon Mijin Mommy Gombe Ya Yi Ikrarin Cewa Da Juna Biyu a Jikinta a Lokacin Da Suka Rabu

A karon farko tun bayan da suka rabu shekara biyu da suka gabata, tsohon mijin jaruma Mommy Gombe, Adam Fasaha, ya yi zargin cewa da juna biyu a jikinta a lokacin da suka rabu, yana mai cewa bai san me ya samu cikin ba bayan rabuwar tasu. Fasaha ya kara da cewa, ya ji zafi sosai kan zargin da ake masa cewa, sai da ya kai tsohuwar matarsa (Mommy) kofar gidansu sannan ya mika mata takardar saki. “A cikin bata min suna da aka yi da bazan manta ba, shi ne cewa, na dakko ta ne na kawo ta kofar gidansu na sake ta.” Fasaha ya ce cikin wata hira da Tashar Tskar gida ta saka a shafin Youtube. Har ya zuwa lokacin hada wannan takaitaccen labari Mommy Gombe ba ta mayar da martani ba kan kalaman na tsohon mijinta ba.

Mommy Gombe (Hoto: Mommy Come Instagram)
Mommy Gombe (Hoto: Mommy Come Instagram)

Har Yanzu Ana Ce-Ce-Ku-Ce Kan Rikicin Zlatan Da DJ Cuppy

A can kudancin Najeriya kuwa, har yanzu tsugune bai kare ba, kan rikicin da ya kunno kai tsakanin mawakiya DJ Cuppy da mawaki Zlatan Ibile. A farkon watan Janairu DJ Cuppy ta yi korafin Zlatan ya toshe ta a kafafen sada zumuntarsa na WhatsApp da Instagram.

Zlatan (Hoto: Zlatan Instagram)
Zlatan (Hoto: Zlatan Instagram)

Hakan ya sa ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, ba ta san me ta ma Zlatan ba tsawon wata tara kenan ya rufe ta ta kafafen sada zumuntarsa .

Amma rahotonni da suka bayyana a baya-bayan nan, sun nuna cewa Zlatan yana fushi da Cuppy ne, saboda ba ta biya sa hakkinsa ba a wakar da suka yi ta “Gelato,” a bara, wacce Cuppy ta gayyato Zlatan. Amma Cuppy wacce diya ce ga hamshakin mai kudin nan Otedola, ta musanta wannan zargi.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG