Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukaddashin Gwamnan Taraba Ya Musanta Yunkurin Tsigeshi


Yozhik, a male Himalayan bear, sits while an employee cools him with a stream of water at the Royev Ruchey zoo on the suburbs of the Siberian city of Krasnoyarsk, Russia.
Duk da raderadin da ake yi cewa 'yan majalisar jihar Taraba na yunkurin tsigeshi daga shugabancin jihar amma shi mukaddashin Alhaji Garba Umar yace shi da majalisar sunan tare suna kuma yin aiki tare cikin lumana.

Mukaddashin gwamnan yace idan ya fito waje sai ya ji ana cewa za'a tsigeshi alhali kuwa suna zaman lumana da 'yan majalisar. Ya sake jaddada kyakyawar dangantaka dake tsakaninshi da majalisar dokokin jihar.

To saidai 'yan majalisar sun dagewa cewa sai an jire duk wanda baya dasawa dasu dake cikin gwamnatin mukaddashin gwamnan. Misali sun bada umurnin a jire shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Ahmed Yusuf Gamaliya . Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Daniel Ishaya ya tabbatar da matsayin majalisar kan batun tsige Gamaliya. Yace duk wanda baya aikinsa yadda ya kamata majalisa zata ce a cireshi. Yace Danbaba Suntai ya kawo Ahmed Gamaliaya ya bashi shugabancin kamfani saka jari. Shi kuma mukaddashin gwamna da ya kama aiki ya bashi shugaban ma'aikatan gidan gwamnati. Yace yawancin wadanda ke Jalingo basu yadda da kasancewar Gamaliya kusa da mukaddashin gwamnan ba.

Batun cewa majalisa take juya mukaddashin gwamna yadda ta ga dama sai Daniel Ishaya yace majalisa ce ta amince Alhaji Garba Umar ya zama mataimakin gwamna. Ita ce ta amince masa ya zama mukaddashin gwamna sabili da haka idan majalisa tace bata yadda da wani kusa da shi ba ai dole ya amince. Idan kuma yaki majalisa tana da karfin ta tilasta masa ya yi abun da zai gamshi al'ummar jihar Taraba. Yace shi mukaddashin gwamna ba dan siyasa ba ne. Domin haka akwai wasu da suke juyashi yadda suka ga dama. Idan majalisa ta ga hakan kuma jihar zata cutu dole ne su gaya mashi ya gyara.

Daga bisani Daniel Ishaya ya ce idan suka ga abun da bai dace ba suka gayawa mukaddashin gwamnan ya gyara, to idan ya ki zasu tureshi gefe guda su kawo wanda zai yi abun da ya kamata.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG