Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Mun Bi Ka'ida Wajen Tattara Sakonnin Email Na Kamfe Din Trump" -inji Mueller


Mai Binciken Trump, Robert Mueller
Mai Binciken Trump, Robert Mueller

A cigaba da murza gashin bakin da ake yi kan binciken zargin hadin baki tsakanin kwamitin yakin neman zaben Shugaban Amurka Donald Trump da kasar Rasha, babban jami'in bincike na musamman Robert Mueller ya kare karbo dubban sakonnin na kwamitin yakin neman zaben Trump da ya yi.

Babban jami’in binciken Amurka na musamman Robert Mueller ya jaddada huruminsa na tattara sakonnin email daga kwamitin yakin neman zaben Donald Trump, kodayake jami’an yakin neman zaben na Trump ba su zo ga sani ba har sai a makon jiya, lokacin da su ka ji cewa wata hukumar gwamnati ta mika ma Mueller sakonnin email din tun watannin da su ka gabata.

Sakonnin email din da ake zance akai sun samu ne daga komfutocin wasu manyan jami’an kwamitin kafa sabuwar gwamnatin Trump 13, kama daga lokacin da aka zabe Trump a farkon watan Nuwamban 2016 zuwa lokacin da ya hau gadon mulki ran 20 ga watan Janairun 2017. Abubuwan da ke ciki sun hada da tattaunawa kan tsaron kasa da kuma abubuwan da Trump zai fi ya su muhimmanci a matakin kasa da kasa, da kuma tantancewar wadanda za a nada a gwamnatin ta Trump.

“Lokacin da mu ka karbo sakonnin email a yayin da mu ke binciken da mu ke kai, au mun samu yaddar mai akwatin email din au mun bi ka’idar da ya kamata mu bi,” abin da mai magana da yawun Mueller ya fada Kenan tunda farko a jiya Lahadi.

Mueller ya tuntubi Hukumar Hidimta Harkokin Gwamnati, wadda ita hukumar gwamnati mai kula da kaddarorin gwamnati, a inda kwamitin yakin neman zaben Trump ya gudanar da harkokinsa, wadda kuma Komfutocinta ne kwamitin ya yi amfani da su, da ta ba shi sakonnin email din. Ba tare da gaya ma kwamitin yakin neman zaben Trump ba, hukumar ta mika ma Mueller sakonnin na email.

Kory Langhofer, wani lauyan kwamitin yakin neman zaben na Trump, ranar Asabar ya gabatar da koke gaban kwamitocin sa ido kan al’amura na Majalisar Dattawa da Wakilai cewa Mueller ya karbo wadannan sakonnin email din, duk kuwa da ya san cewa sakonnin ba mallakin hukumar ba ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG