Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Najeriya Ta Sami Koma Baya A Yaki Da Boko Haram-Ministan Tsaro Janar Mansur Dan Ali Mai Ritaya.


Janar Mansur Dan Ali, Ministan tsaro na Najeriya da daya daga cikin shugabannin Tashar Radio ta Muriyar Amurka John Lansing.

Duk da haka, Janar Dan Ali ya bada tabbacin cewa ba zasu yi kasa guiwa ba wajen kakkabe ragowar 'yan bindigar.

Ministan tsaro na Najeriya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya yarda cewa yakin da dakarun kasar suke da ‘yan binidgar Boko Haram ya sami koma baya, duk da haka yace mayakan kasar ba zasu yi kasa a guiwa ba, wajen ganin sun kakkabe ragowar mayakan ganin cewa sun ci karfin su.

Janar Dan-Ali mai ritaya, ya furta haka ne lokacin da yake magana a bikin "makon ‘yan jarida," da kungiyar ‘yan jarida reshen jahar take shiryawa ko wace shekara.

Shima da yake magana a taron, Gwamnan jahar Borno Kashim Shettima, yace ba dukkan rahotanni bane da ‘yan jarida suke bayarwa suke jin dadinsu ba, duk da haka yace ‘yan jarida sun cancanci yabo kan makomar yaki da ake yi da masu tada kayar ba.

Ana sa bangaren shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya komored Abdulwaheed Olusheli, ya jinjinawa ‘yan jarida wajen yakin ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG