Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Shiga Tsaka Mai Wuya A Jidda - Wasu 'Yan Najeriya Da Suka Je Umrah


‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah.
‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah.

Dandazon ‘yan Najeriya da su ka kammala a umrah, sun makale a filin jirage na Jiddah bayan sun sami cikas din jirgin da zai dawo da su.

Fasinjojin wadanda kamfanin jirgin Max mallakar Dahiru Barau Mangal ya yi jigalarsu suna nuna bukatar daukin gaggawa don wasun su, guzurin su ya kare.

Bayanai na nuni da cewa, da farko an jibge fasinjojin a sashen tashin jirage na kasa da kasa a Jidda inda don yawan su ala tilas Saudiyya ta sauya mu su matsuguni zuwa sashen sauka da tashin alhazai MADINATUL HUJJAJ inda ke da ‘yan wajajen runtsawa.

‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah
‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah

Alhaji Ibrahim Hamza da ke cikin fasinjojin ya ce bayan hatsaniya, hukumomin filin jirgin sun dauke su, su ka kama mu su masaukai a daf da filin.

Kakakin kamfanin jiragen na Max Ibrahim Dahiru ya ce kamfanin ya riga ya dawo da wasu fasinjojin kuma ba lalle ne akwai wani sakaci daga bangaren sa kan halin da ‘yan umrar su ka shiga ba.

‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah
‘Yan Najeriya da su ka makale a Saudiya bayan sun kammala umrah

Yayin da raderadi ke nuna Saudiyya ta dakatar da jigilar ‘yan umrar na Najeriya na wani dan lokaci, fasinjoji sun ce wasu jiragen na tashi zuwa Najeriya ta jirgin Saudi wato Saudi Air.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti

Wasu 'yan Najeriya da suka je Umrah sun makale a Jidda-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

XS
SM
MD
LG