Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Kokarin Sulhu Don A Bar Sheikh Khalid A Mukaminsa Amma Hakan Ya Ci Tura - Imam Usama


Sallah a Masallaci
Sallah a Masallaci

Daya daga limaman masallatan anguwar ‘yan majalisa a Abuja Imam Ibrahim Auwal Usama ya ce sun yi iya bakin kokarin su don hana korar babban limamin anguwar Imam Nuru Khalid amma abun ya gagara.

ABUJA, NIGERIA - Imam Usama wanda ke tabbatar da labarin sallamar Sheikh Khalid bayan tun farko an dakatar da shi, ya ce kwamitin masallatan ya zauna inda sulhun ya juye zuwa matakin kora daga limancin.

Usama ya kara da cewa da alamun wata waya da Malam Nuru a ka ce ya bugo ya na mai cewa in ba a bar shi ya ja sallah a masallacin a jumma’ar nan ba za a samu tashin hankali, hakan ne ya tunzura kwamitin su ka dau matakin mafi tsauri.

Bisa ga bayanai, akwai abubuwa da dama da a ke zargin Malam Khalid da aikatawa da kuma a ke neman dalilin sallamar sa daga limancin.

Duk da haka Ibrahim Usama ya ce ba za a ce bakin alkalami ya bushe ba bisa kara yunkurin sulhu amma dai kwamitin ya riga ya yanke hukunci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya:

Mun Yi Kokarin Sulhu Don A Bar Sheikh Khalid A Mukakaminsa Amma Hakan Ya Ci Tuta - Imam Usama
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG