Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi da Kiristocin Nijar Suna Taron Tabbatar da Zaman Lafiya


Taron tbbatar da zaman lafiya a Nijar

Taron ya shafi duk mutanen fadin kasar da ya hada addinan biyu domin fadakar da mabiyansu mahimmancin zaman lafiya cikin kasar Nijar

Darikar Katolica ce ta tattara malaman addinan biyu a garin Birnin Konni wanda kwatankwacin abun da kungiyar tayi ne a Kenya da Tarayyar Najeriya.

Shugaban addinin Kirista na garin Maradi yayi wa Muryar Amurka karin bayani akan mahimmancin taron. Yace suna taron ne domin musulmi da kiristoci su yi tafiya tare domin a samu zaman lafiya a jamhuriyar Nijar.

A lokacin irin taron ne ita kungiyar Katolika ke kawo tallafi ga mata da samari, mussmman samarin da basu da aikin yi. Su kan hadasu a kungiyance matasan musulmi da kiristoci su yi aiki tare. Suna son su san zaman tare, su yi cudanya da juna da yin annashuwa.

A bangaren mata akan hada kiristoci da musulmai su kafa kungiya kana su kama ma juna tare da ba juna bashi tsakaninsu domin su samu abun yi. Matan suna zuwa bikin juna da suke yi tare domin zaman lafiya.

Kusan shekara daya da ta gabata ne aka fara ganin ana kai hare-hare ga wuraren ibadan kiristoci a Nijar. A kan haka wani babban malamin addinin Islama yayi bayanin abun da suka yi. Yace kusan shekara guda yanzu matasan musulmi da kiristoci da aka dauka suna kasuwanci tare suna kuma aiki tare. Suna cudanya kuma suna daraja juna.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG