Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi 'Yan Kabilar Rohingya Su 12 Sun Halaka A Kogin Naf


Aung San Suu Kyi (d) conversa con el general Zaw Win (i), viceministro de Asuntos Fronterizos, durante el desfile por el Día de las Fuerzas Armadas en Birmania.
Aung San Suu Kyi (d) conversa con el general Zaw Win (i), viceministro de Asuntos Fronterizos, durante el desfile por el Día de las Fuerzas Armadas en Birmania.

Wasu 'yankabilar Rohingya su 12 sun halaka a ciki koginNaf bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife.Wadannanmutanen dai suna kokarin tsrewa ne daga kasar su zuwa Bangladesh.

Musulmi ‘yan kabilar Rohingya su akalla 12 ne suka mutu cikin ruwa a lokacin da kwale-kwalensu dake shake da mutane ya kife jiya lahadi da dare, a lokacin da suke tserewa daga Myanmar don neman mafaka a kasar Bangladesh.

Kwale-kwalen ya nutse a kogin Naf wanda ya raba kasar Myanmar da Bangladesh.

Wani jami’in bakin iyaka na Bangladesh ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa gawarwakin 12 sun hada da na yara 10 da wata tsohuwa da kuma wani magidanci. Yayi hasashen cewa tun da kwale-kwalen ya kife a kusa da Myanmar ne, watakila wasu daga cikin fasinjojin sun iya sun yi ninkaya zuwa bakin gaba.

Jami’ai basu san adadin mutanen dake cikin kwale-kwalen a lokacin da ya nutse ba, amma kuma a yawancin lokuta ana diban mutane fiye da kima cikin irin wannan kwale-kwale.

Daga watan Agusta zuwa yanzu, fiye da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya su rabin miliyan daya sun gudu daga Jihar Rakhine ta Myanmar zuwa Bangladesh

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG